Adadin mamata a girgizar kasar Myanmar ya ka 1,644

Hukumomi a Myanmar sun ce adadin wadanda suka mutu a girgizar kasar ya kai 1,644, yayin da wasu 3,408 suka jikkata, ye zuwa ranar Asabar

Hukumomi a Myanmar sun ce adadin wadanda suka mutu a girgizar kasar ya kai 1,644, yayin da wasu 3,408 suka jikkata, ye zuwa ranar Asabar din nan.

Tunda farko dai mutane 1,007 ne aka sanar sun mutu sai wasu 2,389 da suka jikkata.

Girgizar mai karfi maki 7.7 ta shafi Kasashen Myanmar da Thailand wadanda suk suka ayyana dokar ta baci a ranar Juma’a.

Tuni kasar Myanmar ta nemi taimakon kasashen duniya da kuma kungiyoyi don agazawa wadanda girgizar kasarta shafa.

Kasar Iran ta ce a shirye take ta taimakawa kasashen biyu da girgizar kasar ta shafa.

A wata sanarwa da kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghai ya fitar yau Asabar ya ce Iran a shirye take ta shiga ayyukan agaji da ceto a kasashen biyu.

Baghai ya kuma jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa da kuma gwamnatoci da al’ummomin kasashen biyu.

Ayyukan agaji na kasa da kasa sun fara kwararowa cikin kasar: masu aikin ceto da agaji da suka hada da barguna, kayan abinci da na bincike, daga kasashen China da Indiya da ke makwabtaka da su, da kuma wasu kasashe.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments