Bayanai daga Gaza na cewa adadin Falasdinawan da sukayi shahada mata ne da kananan yara.
Adadin ya hada da kusan falasdinawa 33 da sukayi shahada a cikin sa’o’i 24 da suka gabata sakamakon wani hari da Isra’ila ta kai a wani gida da ke sansanin Nuseirat.
Jiragen yakin Isra’ila sun kai hari kan gidaje da gine-gine da dama a sansanin, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Falasdinu WAFA ya ruwaito.
Rahotanni sun nuna cewa akasarin wadanda aka kashe da kuma jikkata mata ne da kananan yara.
Likitoci sun kuma tabbatar da jikkatar wasu mutane sakamakon harin da wani jirgi ya kai a wani gida da ke kusa da masallacin Yassin a yankin.