Ma’aikatar lafiya a zirin Gaza, ta sanar cewa, adadin mutanen da suka rasa rayukansu sanadin hare haren Isra’ila ya kai 36,586 tun farkon yakin da ake gwabzawa tsakanin Isra’ila da kungiyar gwagwarmaya ta Hamas.
A kalla mutane 36 ne sukayi shahada a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, in ji sanarwar da ma’aikatar lafiya ta kasar ta fitar yau Laraba, inda ta kara da cewa mutane 83,074 sun jikkata a zirin Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba bayan harin ba zata da Hamas ta kai a Isra’ila.
A halin da ake ciki dai kasashen duniya na ci gaba da kira ga bangarorin da su amince tayin yarjejeniyar tsagaita wuta da shugaban Amurka ya sanar.
Ministan Tsaron Isra’ila Yoav Gallant ya ce Ci gaba da tattaunawar sulhu da Hamas kan yarjejeniyar sakin mutane da aka yi garkuwa da su ba za ta dakatar da yakin Gaza ba.
“Duk wata tattaunawa da Hamas za a gudanar da ita ne kawai ta hanyar ci gaba da ba da wuta,” in ji Gallant a wani jawabi da kafafen yada labaran Isra’ila suka watsa.
Amurka dai ta ce Ana ci gaba da dakon martanin kungiyar ta Hamas kan kudirin tsagaita wuta na Joe Biden, kamar yadda mashawarcin Fadar White House kan harkokin tsaro Jake Sullivan ya shaida wa manema labarai.
To saidia Hamas ta ce Isra’ila ce ke kawo cikas kan batun tsagaita wuta.