Adadin Falasdinawan Da Sukayi Shahada A Hare-haren Isra’ila Ya Kai 45,805

Ma’aikatar lafiya ta Falasdinawa ta ce kisan kiyashin da Isra’ila ta yi a Zirin Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 45,805 tare da jikkata

Ma’aikatar lafiya ta Falasdinawa ta ce kisan kiyashin da Isra’ila ta yi a Zirin Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 45,805 tare da jikkata 109,064 tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023.

Ta ce an kashe Falasdinawa 88 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata in ji ma’aikatar lafiya ta Falasdinu a yankin.

Haka kuma mutum 208 suka jikkata a hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai a sassa daban-daban na Gaza, in ji ma’aikatar.

Ma’aikatar ta kuma sake nanata cewa har yanzu akwai gawawwaki da suke makale a karkashin baraguzan gine gine da kuma gefen titina.

Duk da kiraye kirayen da kasashen duniya da kuma kungioyin kasa da kasa ke ma ta Isra’ila na ci gaba da aikata kisan kiyashi a Gaza.

A makonnin da suka gabata kotun hukunta manyan laifuka ya duniya ICC ta fitar da sammacin kame mata firamnistan Isra’ila Benjamin Netanyahu da kuma tsohon ministan yakinsa bisa aikata laifukan yaki a Gaza saidai Isra’ilar ta yi biris da hakan tana mai danganta sammacin da babban abun kunya ga kotun.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments