Search
Close this search box.

Abu Hamzah: Sarayal-Qudus Ba Za Ta Taba Barin Fagen Yaki Ba

Kakakin rundunar “Sarayal-Qudus” ta kungiyar Jihadul-Islami, Abu Hamza ya bayyana cewa’ Farmakin da su ka kai a Janin ya yi nasara, don haka ba za

Kakakin rundunar “Sarayal-Qudus” ta kungiyar Jihadul-Islami, Abu Hamza ya bayyana cewa’ Farmakin da su ka kai a Janin ya yi nasara, don haka ba za su taba barin fagen dag aba.

Abu Hamzah ya bayyana cewa; Mayakan nasu sun yi nasarar tarwatsa motocin yakin HKI guda biyu a wani kwanton bauna da su ka yi musu a yankin “ Maraj Bin Amir da hakan ya yi sanadin kashe sojojin da suke ciki da kuma jikkata wasu.

Kakakin rundunar “Sarayal-Qudus” ya kara da cewa; An dauki sa’oi 8 ana tun bata –kashi a tsakaninsu da sojojin mamaya da su ka yi kokarin yin kutse a cikin sansanin ‘yan hijira na Jenin.

Tun da fari, sojojin mamayar HKI sun sanar da cewa an kashe musu wani jami’in soja kuma kwamandan runduna da kuma raunana wasu 16.

 Kafafen watsa labarun HKI sun bayyana abinda ya faru da cewa; ba abu ne mai sauki ba.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments