Ministan harkokin wajen Iran Amir Hussain Abdullahiya ya ce; kai wa karamin ofishin jakadacin Iran da Syria hari, ketare duk wata iyaka ce ta dokoki da yarjeniyoyin duniya.
Ministan harkokin wajen na Iran,Amir Husain Abdullahiyan ya kuma kara da cewa kuma HKI ce za fuskanci mummunan sakamakon abinda ta aikata.
Ministan harkokin wajen na Iran ya kuma ce; Saboda Netenyahu ya ci kasa a Gaza, ya rikice.
Amir Abdullahiyan ya kuma yaba wa ministan harkokin wajen Syria Faysal Mikdad wanda ya ziyarci ofishin jakadanin Iran a birnin Damascuss inda ya bayyana alhininsa akan abinda ya faru.