Babban hafsan hafsoshin rundunar dakarun Iran,”Manjo Janar na sojan sama, Ali Abdullahi ya yi kira da gargadi ga kasashen wannan yankin akan bai wa Amurka duk wani irin taimako domin hakan yana a matsayain yin tarayya da su a cikin yaki.
Kamfanin dillancin labarum “Irna” na Iran ya nakalto manjo janar Abdullahi yana rubuta wannan gargadin a shafinsa na sadarwa yana mai cewa: “Ya kamata kasashen dake kudancin tekun pasha a kodayaushe suke bayyana cewa ba su bai wa Amurka kasarsu ta kawo mana hari, su kwana da sanin cewa babu wani abu wanda yake shigar mana duhu.”
Haka nan kuma ya ce; Babu yadda za a yi a ce tarin jiragen yaki,musamman jiragen tankokin mai da suke a cikin kasashensu, ba tare da sanin wadannan kasashen ne ba.”