A wata kasida da jaridar Guardian ta wallafa ta kawo cewa ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi ta bayyana cewa iran ba za ta taba watsi da hakkinta na mallakar fasahar nukiliya ba, kuma ashirye take da duk wani mataki na diflomasiya, kuma ya jaddada cewa tattaunawa yasha banban da tsara yadda za’a yanke hukumci
Wadannan kalamai suna zuwa ne bayan da shugaban Amurka Donald Trump yayi barazanar cewa idan iran ta ci gaba da kera makamai to babu abin da ya ragewa Washington banda ta kawo karshensa cikin gaggawa, wadanan kalamai suna da hadari babba na daukar matakin soji, wannan ya sanya iran take mayar da martani a shafin yanar gizo na kasashen yamma.
Takaddama tsakanin iran da Isra’ila ta kara tsami sosai musamman a yan shekarun baya bayan nan,da ya kai ga Amurka ta kai hari kai tsaye a iran a watan yunin shekara ta 2025, isra’ila ta bayyana hujjar kai harin saboda damuwar da take da shi kan shirin nukiliyar iran, ba wai wuraren soji ba kawai har ma da masana kimiyya da ma fararen hula.
Shugaban Amurka trump ya bayyana cewa Amurka ta taka rawa sosai wajen taimakawa bangarorin hare-haren da aka kai,