Abbas Araqchi: Alatilas ne Netanyahu ya amince da batun dakatar da yaki a Lebanon

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya jaddada cewa, an tilastawa firaministan haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu tsagaita bude wuta a Lebanon, bayan da

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya jaddada cewa, an tilastawa firaministan haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu tsagaita bude wuta a Lebanon, bayan da ya fuskanci asara mai yawa a kudancin kasar ta Lebanon, har’ila yau, duk tare da cikakken goyon bayan da ya samu daga kasar Amurka.

Araghchi ya yi nuni da cewa, Hizbullah ta sake wargaza shirin Haramtacciyar Kasar Isra’ila, inda ta kasa cimma manufofin da ta zayyana a matsayin abin da take son cimmawa a wannan yaki, mafi muhimmanci daga cikisu  shi ne wargaza kungiyar Hizbullah, da kwance makamanta baki daya.

Baya ga haka kuma haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana dawowar yahudawan da suke zama matsugunnasu a arewacin Falastinu da aka mamaye, a matsayin daya  daga cikin manufofin yaki kan kasar Lebanon.

Ministan y ace gabata cewa Haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta cimma ko da daya daga cikin wadannan manufofi ba, domin kuwa ba ta iya wargaza Hizbullah ko makamanta ba, kamar yadda kuma ba ta iya kare kanta daga makaman Hizbullah har zuwa ranar fara aiwatar da yarjejeniyar dakatar da yakin ba, kamar yadda kuma ba ta iya mayar da Yahudawan da hizbullah ta kora daga matsugunnasu a arewacin kasar ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments