Shugaban hukumar zabe na kasar Iran Cahhchiraqi ya sanar da cewa da akwai wadanda su ka cancanci yin zabe su miliyan 61 da dubu dari 352 sa 321.
Shugaban hukumar zaben ta Iran ya kuma ce;Da akwai bukatar duk wanda zai kada kuri’ar ya gabatar da takardunsa na dan kasa, bayan tanatancewa zai ya kada kuri’a.
Da misalin karef 8;00 na safiyar yau Juma’a ne dai aka bude mazabu a fadin kasar domin bai wa mutane dama zabar shugaban kasa.
Wannan zaben dai ya zo ne bayan shahadar shugaban kasa Ibrahim Ra’isi a ranar 19 ga watan Mayu a wani hatsarin jirgin sama maras matuki.
Tuni jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kada ta shi kuri’ar a Husainiyar Imam Khumaini dake birnin Tehran.