Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arakci ya isa birnin Doha na kasar Katar domin halartar taron da zai hada kasashen Turkiya, Rasha da mai masaukin baki Katar.
Taron na Katar zai mayar da hankali ne wajen lalubo hanyoyin sulhu da zaman lafiya akan rikicin kasar Syria.
A yayin wannan taron dai za a yi ganawar bayan fage a tsakanin ministan harkokin wajen Iran da kuma na kasar Turkiya Hakan Faidan domin farfado da yarjejeniyar Astana.
Tun a 2017 ne dai aka fara tattaunawa a Astana a kasar Khazakistan wacce ta kai ga tsagaita wutar yaki a kasar ta Syria, kafin kuma yanzu yaki ya sake barkewa.