Mahukunta a New Orleans a Amurka sun sanar da cewa mutane 10 sun mutu, yayin da wasu 30 su ka jikkata sanadiyyar taka su da mota da aka yi a daidai lokacin da ake yin bikin sabuwar shekara.
Kafafen watsa labarun Amurka sun ambaci cewa mutane da dama ne su ka mutu bayan da wani mutum ya take su da mota a titin Bourbon dake unguwar Faransa a garin New Orelans a yau Laraba.
Shedun ganin ido sun ce wata babbar motace da take gudu ta bi ta kan mutanen da suke bikin sabuwar shekara, sannan kuma matukin motar ya fito da bindiga ya bude wuta akan mutanen. ‘Yan sanda da suke a wurin sun mayar wa da matukin motar wuta.
Tashar talabijin din IBC ta ambato ‘yan sanda suna cewa, da gangan ne matukin motar ya take mutanen ba hatsari ba ne.
An kai wanann harin ne dai a daidai lokacin da birnin yake shirin karbar bakuncin wasan kwallon kafa na zumunta da ake yi a kowace shekara a jami’ar Georgia.