Sojojin mamayar HKI suna cigaba da yi wa al’ummar Falasdinu kisan kiyashi a cikin sassa daban-daban na zirin Gaza.
Da safiyar laraba Falasdinawa 8 sun yi shahada sanadiyyar hare-hare da jragen yakin HKI su ka kai wani gida dake Jabaliya a arewacin Gaza.
Bugu da kari sojojin mamayar suna kai wasu hare-haren akan asibitin “Kamal –Adwan” wanda shi ma yake a arewacin Gaza.
A kudancin Gaza kuwa sojojin HKI sun kai hari akan wani gida dake yankin Ma’ana, a gabashin garin Khan-Yunus, da hakan ya yi sanadin shahadar mutane 10.
An kuma sami wasu shahidan biyu a unguwar “al-manarah” dake kudancin Khan-Yunus, bayan hari akan kidan mutane. Har ila yau HKI ta kai hari akan hemar da take dauke da ‘yan hijira da ta rusawa gidaje, a unguwar al-mawasi, da shi ma ya yi sanadiyyar shahadar mutane 5.
Isra’ilan dai tana son korar mutane arewacin Gaza ne daga gidajensu da tilasta musu barin yankin domin ta kafa shinge na kariya tsakaninta da Falasdinawa.