Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya musanta zargin kasar Iran da kai hare hare da Drones kan Kuwait.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Aragchi na fadar haka a lokacinda yakezantawa da tokwaransa na kasarKuwait Sheikh Jarrah Jaber Al-Ahmad a jiya Alhamis.
Aragchi ya kara da cewa, gwamnatin kasar Iran a shirye take ta hada kai da gwamnatocin kasashen Kuwai da Italia don gano daga inda wadannan jiragen Drones suka fito.
Ministan ya kara jaddada cewa, gwamnatin kasar Iran bata da hannu a hare haren da aka kaiwa kasar Kuwait tare da amfani da makaman Drones ajiya ALhamis. Ya kuma bukaci aiki tare da gwamnatin kasar Kuwait don gano da kuma tabbatar da wadanda suka kai hare haren daga kuma daga inda suka cilla makaman. Har’ila yau, ministan ya zanta da ministan harkokin wajen kasar Italia Antonio Tajani inda ya jajanta masa mutuwar yan asalin kasar Kuwaita guda biyu a hare haren makaman Drones kan kasar Kuwait. Ya kuma musanta samun hannun Iran a hare haren.