Ayatullahi Larijani: Al’umma Su Ne Kashin Bayan Tsarin Kasa

Al’umma su ne ma’abuta juyin juya halin, za a iya dogara da ikonsu wajen magance matsalolin ƙasa Shugaban Majalisar Fayyace Masalahar Tsarin Musulunci Ayatullahi Sadiq

Al’umma su ne ma’abuta juyin juya halin, za a iya dogara da ikonsu wajen magance matsalolin ƙasa

Shugaban Majalisar Fayyace Masalahar Tsarin Musulunci Ayatullahi Sadiq Amoli Larijani ya jaddada rawar da mutane ke takawa a kafa da kuma ci gaba da gudanar juyin juya halin Musulunci, yana mai cewa: “Mutane ne masu dauke da ruhin juyin juya halin, don haka za a iya dogara da iyawarsu don magance matsalolin kasar.”

A cewar kamfanin dillancin labaran Mehr, Ayatullah Sadiq Amoli Larijani, shugaban Majalisar Fayyace Masalahar Tsarin Musulunci ta Iran a cikin wani sako da aka buga a shafin yanar gizonsa a Makon Dakarun Sa-Kai na kare juyin juya halinMusulunci “Basij”, ya nuna muhimmancin amincewa da kai a cikin akidar Dakarun Basij, yana mai cewa: “A cikin wannan akida, amincewa da kai ya samo asali ne daga mahangar tauhidi. Ta hanyar ambaton Allah, mutum yana gane darajarsa, matsayinsa da alhakinsa, kuma yana cika aikinsa a kowane fage da ruhin jihadi da nufin kusantar Allah Madaukakin Sarki.”

Yana mai nuni da rawar da Imam Khomeini ya taka wajen kafa Dakarun Sa-Kai na Basij: Yana mai jaddada cewa: Imam Khomeini ya bai wa mutane fagen, wadanda su ne masu juyin juya halin da kuma kashin tsarin Musulunci.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted