Majiyar Soji: Zabe Sai Bayan Shekaru Biyu A Kasar Guinea-Bissau

Guinea-Bissau ta dage zaɓe da shekaru biyu zuwa shekarar 2028 Shugabannin mulkin soja na Guinea-Bissau sun dage zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa zuwa

Guinea-Bissau ta dage zaɓe da shekaru biyu zuwa shekarar 2028

Shugabannin mulkin soja na Guinea-Bissau sun dage zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa zuwa nan da shekaru biyu masu zuwa, wanda hakan ya jinkirta wa’adin da kasar ta dauka na komawa kan mulkin farar hula.

A cikin wata doka, shugaban rikon kwaryar kasar Janar Horta N’Tam ya ambaci rashin kayan aiki na fasaha, kayan aiki da kudi da ake bukata don tabbatar da zabe mai inganci.

Sanarwar ta zo daidai shekara guda bayan da sojoji suka kwace mulki, suka hambarar da Shugaba Umaro Sissoco Embalo tare da dakatar da tsarin zabe.

Tun daga lokacin, gwamnatin sojan ta kuma aiwatar da sauye-sauye a tsarin mulkin kasar wadanda ke karfafa ikon shugaban kasa, duk da kiran da ‘yan adawa suka yi na kaurace wa tsarin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted