Isra’ila Ta Kashe Wani Babban Jami’in Tsaro Na Gaza Da Matarsa

Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza ta yi tir da kissan wani babban jami’in tsaro na cikin gida a yankin a wani hari

Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza ta yi tir da kissan wani babban jami’in tsaro na cikin gida a yankin a wani hari da ta kai kan gidansa a yau Laraba, inda ta kashe shi da matarsa da kuma yayansu 2.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Hamsa a Gaza na cewa, kissan Mohammad Abuluf ya nuna cewa isra’ila tana ci gaba da kissan kiyashi a gaza, irin kissan da ya haramta bisa dokokin kasa da kasa.

A safiyar yau Laraba ne, wasu makamanIsra’ila suka fada a kan gidan Mohammad Abu luf da ke unguwar Al-shati dake cikin birnin Gaza a bakin ruwa, inda suka kashe shi da matarsa da kuma yayansa biyu.

Labarin ya kara da cewa wannan yana faruwa ne a dai dai lokacinda ake cikin abinda suke kira yarjeniyar zaman lafiya. Wannan Isra’ila bata taba mutuntashi bat un lokacin da aka rattaba mata hannu a cikin watan Octoban shekara ta 2025.

Mafi yawan manya manyan kasashen duniya sun yi shiru kan abinda yake faruwa a Gaza, na hana kayakin agaji isassu ciga yankin da kuma ayyukan jinkai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted