Iran Ta Karyata Cewa Za Ta Mika Tataccen Sanadarin “Uranium” Zuwa Waje

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Dr. Isma’ila Baka’i, ya bayyana cewa; Babu yadda za a fitar da sanadiyar Uranium na Iran zuwa wajen kasar.  A

Iran : bukatun Amurka marar kan gado ne suka hana a cimma yarjejeniya

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Dr. Isma’ila Baka’i, ya bayyana cewa; Babu yadda za a fitar da sanadiyar Uranium na Iran zuwa wajen kasar.

 A wata hira da tashar talabijin ta kasar Iran, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran din ya ce’ ko kadan babu gaskiya a cikin batutuwan da suke fitowa daga bakunan wasu jami’an gwamnatin Amurka na cewa za a fitar da sanadarin urani’um daga kasar Iran’ sannan ya kara da cewa; Babu yadda za a yi mu amince da fitar da tataccen sanadarin uranium zuwa waje ta kowane yanayi, kuma kamar yadda kasa ta Iran take da tsarki a wurinmu, haka nan wannan batun yake da muhimmanci a wurinmu.”

Dr.Baka’i ya ce; ko kadan ba mu bijiro da batun mika tataccen sanadarin uranium ga Amurka ba,amma da akwai wasu shawarwari masu yawa da aka bijiro da mu akan batun.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted