Mataimakin shugaban cibiyar kasuwanci ta Iran, ya sanar da cewa za a yi bikin baje koli na manyan kamfanonin Iran na shekara-shekara daga ranar 18 zuwa 22 ga watan na Yuni.
Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya nakakto Amir Rosha Pakhs yana Magana akan muhimmancin wannan baje-kolin wanda daya ne daga cikin muhimman ayyukan na kasuwanci a cikin kasar, domin yana nuni da karfin kayan kasuwancin Iran da ake fitar da su kasuwannin waje.
Haka nan kuma ya yi Ishara da yadda a wurin baje-kolin ake son mayar da hankalin akan kere-keren da Iran take yi nesa da man fetur da dangoginsa, da kuma karafa hanyoyin yin kasuwanci da kasashen waje.