Sojojin Siriya Sun Bada Sanarwan Mamaye Birnin Tabaqah Da Kuma Madatsar Ruwa Ta Furat

Ma’aikatar tsaron kasar Siriya ta bada sanarwan samun  cikekken iko a kan tashar jiragin sama na Tabaqah ta sojoji da ke wajen birnin Riqqah a

Ma’aikatar tsaron kasar Siriya ta bada sanarwan samun  cikekken iko a kan tashar jiragin sama na Tabaqah ta sojoji da ke wajen birnin Riqqah a arewacin kasar Siriya.

Tashar talabijin ta Al-Mayaddeen ta kasar Lebanon ta nakalto majiyar kungiyar kurdawa ta ‘Kasad’ tana cewa sun fafata da sojin Damask a wajen birnin Riqqah.

Gwamnatin Siriya ta kara da cewa ta kwace iko da wadan nan yankuna a hannun kungiyar ‘raya democradiyya ta Siriya wato ‘Kasad’ sun kuma kace wasu wurare daga hannunsu, amma sun gano cewa mayakan Kasad sun kashe fursinoni da fursinonin yaki da dama a garin Tabaqah kafin su fice daga yankin.

Kimani wata guda kenen sojojin gwamnatin Siriya da kuma na kungiyar kurdawa mai neman bellewa daga kasar Siriya suka yi ta fafatawa a tsakaninsu don tabbatar da ikonsu a arewacin kasar ta Siriya.

Banda haka sojojin Julani sun ce sun kama mutane 30 a garin Tabaqah wadanda suke kokarin tada hankali, sun kuma kaisu inda ya dace da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted