Asusun kula da yara na MDD, wato Unicef, ya bayyana cewa yara sama da 100 ne suka rasa rayukansu tun bayan cimma yarjeejniyar tsagaita wuta a Gaza.
Tun lokacin da aka fara tsagaita wuta a ranar 10 ga Oktoba, 2025, an kashe yara sama da 100 a Gaza, kwatankwacin kusan yaro daya a kowace rana inji Unicef.
Har yanzu lamarin rayuwa bai daidaitu ba a Gaza inji kungiyoyin agaji, duk da cewa hare –haren bama-bamai da harsasai sun dan ragu a lokacin tsagaita wutar, amma ba su tsaya ba.
Yawaicin mace macen na faruwa ne ta hanyar hare-haren jiragen sama da jiragai masara matuka, ” in ji James Elder, mai magana da yawun UNICEF, a lokacin taron manema labarai na yau da kullun na Majalisar Dinkin Duniya a Geneva.
Mista Elder ya jaddada cewa karin yara sun mutu sakamakon yanayin hunturu mai tsanani.
A saboda haka UNICEF, ta bukaci a bude hanyoyin samun taimako, kara yawan kwashe yara daga yankin, da kuma tabbatar da cewa wannan shi ne “lokacin da kisan yara a Gaza zai kare.”