Babban magatakardar majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr.Ali Larijani ya tattauna ta wayar tarho da Fira ministan kasar Qatar, kuma ministan harkokin wajenta Muhammad Bin Abdurrahman al-Thani akan abubuwan da suke faruwa a cikin wannan yankin na yammacin Asiya.
A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar Qatar ta fitar ta ce, bangarorin biyu sun tattauna hanyoyin bunkasa alaka a tsakaninsu da kuma sauran batutuwan da suke da muhimmanci a wurinsu.
A gefe daya, Dr. Ali Larijani ya tattauna ta wayar tarho da babban mai bai wa gwamnatin Iraki shawara akan harkokin tsaron kasa.
Al-A’araji ya yi wa Allah godiya akan nasarar da Iran ta samu, ta bayannan, yana mai kara da cewa; makiya ba su san cewa al’ummar Iran za ta hada karfi da karfe wuri daya ba, domin tabbatar da hadin kai a tsakaninsu.
Haka nan kuma ya ce; Al’ummar Iraki da al’ummar Iran suna tafiya ne akan tafarki daya, don haka wannan nasarar da Iran ta samu tamu ce.