Larijani : Trump ne ke da alhakin zubar da jinin Iraniyawa

Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran ya yi watsi da barazanar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa al’ummar kasar, yana mai bayyana shi

Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran ya yi watsi da barazanar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa al’ummar kasar, yana mai bayyana shi a matsayin daya daga cikin manyan wadanda suka aikata kisan gilla a Iran.

Ali Larijani yana mayar da martani ne ga wani sako da Trump ya wallafa a shafukan sada zumunta yana kira ga masu zanga-zangar da su “karbe cibiyoyin gwamnati” kuma yana mai cewa “taimako yana kan hanya.”

Ya yi ta bayyana goyon bayansa ga zanga-zangar sau da yawa kuma ya yi barazanar kai hari kan Iran idan aka kashe abin da ya kira “masu zanga-zangar lumana”.

“Mun ayyana sunayen manyan masu kisan gillar al’ummar Iran: 1- Trump 2- Netanyahu,” in ji Larijani a wani rubutu da ya yi.

Yana magana ne game da harin da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran a watan Yunin 2025 na kwanaki 12, wanda ya kashe ‘yan Iran sama da dubu a fadin kasar tare da lalata kayayyakin more rayuwa na farar hula, sojoji, da kuma cibiyoyin nukiliya.

A ranar Talata, wani babban jami’in ‘yan sanda ya ba da rahoton cewa an tsare akalla ‘yan daba 297 da ke da hannu a lalata kadarorin gwamnati da kadarorin jama’a.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted