A ci gaba da gasar cin kofin kwallon kafa na Afrika da yanzu haka ke gudana a Morocco, Gabon ta doke Mozambique 3-2, yayin da Sudan ta doke Equatorial Guinea da 1-0 a wasansu na ranar Lahadi.
Haka zalika Aljeriya da doke Burkina faso 1-0 sai kuma Ivory Coast ta yi kunnen doki 1-1 da Kamaru.
Ranar Litini akwai karawa tsakanin Zimbabwe da Afrika ta Kudu, Haka kuma akwai fafatawa tsakanin Angola da Masar.
Akwai kuma karawa tsakanin Zambia da Morocco mai masaukin baki.
A yayin da Mali zata fafatawa da Comoros.