WHO ta yi gargadi game da sake fuskantar barazanar malaria

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi gargadin cewa za a iya fuskantar mummunan barazanar zazzabin cizon sauro, musamman a nahiyar Afirka.   Yara sun

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi gargadin cewa za a iya fuskantar mummunan barazanar zazzabin cizon sauro, musamman a nahiyar Afirka.  

Yara sun fi fuskantar rauni, yayin da ake fuskantar cikas ga kawar da cutar.

Kasashen da suka fi fuskantar mummunan mace-mace da ke da alaka da zazzabin cizon sauro, a Afrika su ke inji rahoton

A shekarar 2024, an sake fuskantar dawowar zazzabin cizon sauro a duniya, inda aka kiyasta mutuwar mutane 610,000.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta jaddada cewa Afirka ta kasance yankin da cutar ta fi shafa, wanda ya kai kashi 95% na mace-mace masu nasaba da cutar.

Kuma wannan yanayin da ba a saba gani ba yana shafar yara ‘yan kasa da shekara biyar, wadanda ke wakiltar kusan kashi 76% na mace-macen da aka samu a nahiyar.

Kasashen na Afrika da lamarin ya fi shafa su ne a sahun gaba  Najeriya, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo (DRC), da Nijar.

Najeriya ce ke da mafi yawan mace-macen da ke da alaƙa da zazzabin cizon sauro, inda kashi 31.9%, sai Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da kashi 11.7%, sannan Nijar da kashi 6.1%.

Wannan na da nasaba ne sakamakon gibin kudi mai yawa.

A shekarar 2024, an ware dala biliyan 3.9 don shawo kan cutar maleriya, kasa da rabin abin da aka sa gaba na dala biliyan 9.3 a shekarar 2025.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted