Hukumar Agaji mai kula da Falasdinu dake karkashin MDD, ( Unrwa) da ta fitar da wannan alkaluman na yawan gidajen da ‘yan mamaya su ka rushe, ta kuma kara da cewa; Da akwai dubban iyalai Falasdinawa da suke raywua a cikin hemomi kuma a cikin mawuyancin yanayi, ga shi kuma sanyi yana karatowa.
Hukumar ta Agaji ta kuma sanar da cewa; Ta dogara ne da bayanai da ake amfani da su wajen raba kayan agaji da kai tsaye MDD take da hannu a ciki tare da aikin hadin gwiwa da kungiyar “Red Corss” da kuma kungiyar “Red Crecent”.
Unrwa ta kuma ce; Tana aiki a tare da sauran kungiyoyin agaji wajen rabawa iyalan Falasdinawa kayan agaji.