Gwamnatin Najeriya Ta Sanar Da Sabon Sharadi Na Bude Asusun Banki

Gwamnatin Tarayya ta sanar cewa Samun Lambar Tantance Haraji (Tax ID) zai zama wajibi ga duk ƴan  Nijeriya da ke hulda da bankuna da sauran

Gwamnatin Tarayya ta sanar cewa Samun Lambar Tantance Haraji (Tax ID) zai zama wajibi ga duk ƴan  Nijeriya da ke hulda da bankuna da sauran ayyukan hada-hadar kudi daga ranar 1 ga Janairu, 2026.

Wannan sabon umarni yana cikin Dokar Gudanar da Haraji ta Nijeriya, 2025, wacce shugaban kasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kwanan nan. A karkashin Sashe na II, bangare na 4 na dokar, dukkan mutane da kungiyoyi da abin da haraji ya shafa dole ne su yi rajista a hukumomin haraji da suka dace kuma su samu Katin Tantance Haraji (Tax payer Identification Card).

Dokar ta ba hukumomin haraji ikon bayar da Tax ID a madadin wadanda suka gaza yin rajista, ko su ki karbar bukata idan bayanan da ake da su sun nuna hakan ya dace. Dole ne a sanar da mai nema duk wata cikin kwanaki biyar na aiki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted