Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa, har yanzu ba a warware makomar sinadarin uranium da aka inganta da ya kai kashi 60 cikin 100 ba, yana mai cewa an adana kayayyakin a cibiyoyin makamashin nukiliyar da aka kai harin.
A wata hira da jaridar Financial Times ta kasar Birtaniya, Araqchi ya ce har yanzu ana ci gaba da tantance barnar da aka yi a cibiyoyin makamashin nukiliyar, kuma samun damar shiga wasu wuraren da abin ya shafa na da matukar wahala, lamarin da ya sa ba a san makomar uranium sama da kilogiram 400 ba.
Dangane da tambayar ko an cire muhimman kayan aikin cibiyoyin kafin a kai harin? Araqchi ya amsa da cewa: “Ya aike da wasika zuwa ga Grossi (Daraktan Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya) cewa Suna iya daukar matakan kare kayayyakin cibiyoyin makamshin nukiliyarsu, amma a zahiri bai ce sun cire su ba.
Ya yi nuni da cewa: Uranium din akwai yiwuwar ya samu matsala ko kuma an tarwatsa shi, amma har yanzu ba a kammala tantancewar karshenmakamarsa ba.