An Bude Juyayin Ashura A Fadin Iran

A ranar farko ta watan Muharram, an bude juyayin Ashura ta hanyar yin taron kananan yara a matsayin nuna  juyayi ga jaririn Imam Hussain          (

A ranar farko ta watan Muharram, an bude juyayin Ashura ta hanyar yin taron kananan yara a matsayin nuna  juyayi ga jaririn Imam Hussain          ( a.s)  Ali Asgar ( a.s) da abokan gaba su ka kashe a Karbala.

Iyaye mata dauke da kananan yaransu  masu watanni  6 daga  haihuwa sun cika wurare mabanbanta na Iran suna masu mika juyayinsu na shugaban Shahidai Imam Hussain ( A.S).

Bugu da kari iyaye matan sun gargadi HKI da Amurka akan fada da Iran, suna masu cewa; Dukkanin ‘ya’yansu da za su girma za su kasance sojojin Imamul Hujja ( a.s) da za su yake su.

Baya ga Iran da akwai kwasu kasashe 45 da ake juyayin Ashura a duniya.

Taro mafi girma na juyayin Ashuda din shi ne na hubbaren Imam Riza     ( a.s) dake birnin Mashhad. Adadin wuraren na juyayin Ashura na kananan yara sun kai 700 a cikin birane da kauyukan Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted