Jagoran Juyin Musulunci: Wajibi Ne Al’ummar Iran Su Sa Abokan Gaba Yanke Kauna

A jawabin da ya gabatar ga al’ummar Iran a yau Litinin, jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya ce; A kowace shekara

A jawabin da ya gabatar ga al’ummar Iran a yau Litinin, jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya ce; A kowace shekara al’ummar Iran suna bayyana girman matsayinsu a daidai lokacin da ake tuna zagayowar ranar cin nasarar juyin musulunci ta 22 ga watan Bahman na hijira shamshiyya, wanda ya yi daidai da 11 ga watan Febrairu.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya fada a cikin jawabinsa da aka watsa ta kafafen watsa labaru cewa; Al’ummar Iran tana cike da kumaji da tsayin daka, da kuma cika alkawali, kuma tana sane da abubuwan da suke amfanarta da masu cutar da ita.

Jagoran juyin musulunci na Iran din ya kuma ce; A cikin wannan rana ta cin nasarar juyin musulunci, al’ummar Iran sun sami gagarumar nasara mai girma, domin sun tseratar da kawukansu da kuma kasarsu daga tsoma bakin ‘yan kasashen waje.” Haka nan kuma ya ce, ‘yan kasashen wajen sun yi kokarin sake mayar da hannun agogo baya a kasar a tsawon shekaru, amma tsayin dakar al’ummar Iran ya hana su.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma ce; Karfin Iran a matakin farko shi ne al’ummarta kafin akai ga yin Magana ga makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuki,kuma abin a yi wa Allah godiya ne, al’ummar suna ci gaba da yin tsayin daka da turjiya.

Jagoran juyin musuluncin na Iran ya ce,da yardar Allah matasan kasar Iran za su ci gaba da samar da ci gaba a cikin fagage na ilimi, taqawa, kere-kere da tarbiyya da zai karawa Iran abubuwan alfahari.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted