Jiridar Sunday Times ta habarto cewa; Dubban ‘yan gudun hijiran Sudan ne suke cikin halin kakani ka -yi a sansanin ‘yan gudun hijiran kasar Chadi
A garin Adré na Chadi, da ke kan iyaka da yankin Darfur na Sudan, ɗaya daga cikin bala’o’in jin kai mafi girma a duniya yana faruwa, a cewar jaridar The Sunday Times ta Birtaniya.
Babbar wakiliyar jaridar daga ƙasashen waje, Christina Lamb, ta ba da rahoto game da abin da ta gani da idonta a wannan gari na kasar Chadi, inda wani sansani na wucin gadi ya ƙunshi ‘yan gudun hijira sama da 160,000 ‘yan Sudan, galibi mata da yara, waɗanda suka bazu a kan tuddan yashi. Sun tsere daga yaƙin da ke zubar da jini da ya doshi tsawon shekara ta huɗu, suna guje wa kisan kare dangi, fyaɗe, yunwa, da kuma fuskantar Rashin duk wani abin more rayuwa na yau da kullun.
A cewar jaridar, Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa sama da ‘yan Sudan miliyan daya ne suka tsallaka zuwa Chadi tun bayan barkewar yaki a watan Afrilun shekara ta 2023, bayan da birane da garuruwa a yankin Darfur suka rikide suka zama wuraren kisan gilla ga jama’a.