Gaza : Yaran Falasdinawa 37 Isra’ila ta kashe tun farkon wannan shekara

Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ruwaito cewa akalla yara 37 ne suka mutu tun farkon shekarar nan ta 2026 a

Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ruwaito cewa akalla yara 37 ne suka mutu tun farkon shekarar nan ta 2026 a hare-haren da Isra’ila ta kai a Zirin Gaza.

Daraktan UNICEF a yankin na Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka Edouard Beigbeder, ya ce lamarin ya ci gaba da zama “mai matukar hatsari ga yara da yawa a Zirin Gaza, duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da ta fara aiki a watan Oktoban 2025.

A watan Janairu, mai magana da yawun UNICEF James Elder ya bayyana cewa an kashe yara sama da 100 na Falasdinawa, ciki har da yara maza 60 da ‘yan mata 40, a Gaza tun lokacin da aka fara tsagaita wuta a watan Oktoban 2025.

” A halin yanzu, Elder ya nuna mummunan tasirin hare-haren Isra’ila kan sha’anin ilimi a Gaza, inda kusan kashi 90 cikin 100 na makarantu suka lalace, wanda ya bar yara sama da 700,000 ba tare da samun damar zuwa karatu akai-akai ba.

Isra’ila ta kaddamar da kisan kare dangi a Gaza a ranar 7 ga Oktoba, 2023, inda ta kashe Falasdinawa sama da 72,027, galibi mata da yara, tare da raunata wasu sama da 171,651.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted