Mai Magana da yawun ma’aikatar tsaron Iran Kanar Riza Talayi Nik, ya bayyana cewa; Saboda dalilai na tsaro, ba su bayyana nau’oin makaman da aka kera ba, saboda mu bayar da mamaki.
Kanar Talayi ya bayyana hakan ne dai a yayin da yake yaye kallabin wasu daga cikin kere-keren na Iran a fagen tsaro a yau Litinin, daga ciki har da jirage marasa matuki da aka kaddamar domin amfani da ita a cikin fagen ayyukan agaji.
Kanar Talayi ya kuma ce; Kirkirarriyar fasaha tana taka gagarumar rawa wajen kera kayan aiki a fagen tsaro, shi ne ya sa ma’aikatar tsaro take kokarin amfani da shi domin bunkasa ayyukanta.
Haka nan kuma ya ce; Cibiyar da take kula da jirage marasa matuki dake karkashin ma’aikatar tsaro, za ta fara bayar da taimako ga kamfanoni masu zaman kansu domin su ci moriyar matakan da za su dauka na tsara da kera jiragen.
Kakakin ma’aikatar tsaron ta Iran ya kuma ce; Muna tsammanin sabuwar shekarar da za a shiga ta hijira shamsiyya ta zama ta bunkasa amfani da jiragen sama marasa matuki, a cikin fagagen da ba na soja ba.