Iran ta musanta rahotanni shirin zartar da hukuncin Kisa kan wani dan zanga zanga

hukumomin shari’a na Iran sun musanta rahotannin dake cewa ana shirin aiwatar da hukuncin kisa kan wani matashi da aka kama cikin bata-gari da aka

hukumomin shari’a na Iran sun musanta rahotannin dake cewa ana shirin aiwatar da hukuncin kisa kan wani matashi da aka kama cikin bata-gari da aka kama yayin zanga zangar lumana da makiya suka rura ta rikide zuwa tarzoma a kasar.

An kama Erfan Soltani, mai shekaru 26, a ranar 10 ga Janairu a lokacin tarzomar, kuma an tuhume shi da hannu a tayar da tashin hankali a kasa,” da kuma “ayyukan farfaganda” kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta wallafa, a cikin wani sako da aka buga a harshen Farisanci a shafin X, cewa za a kashe Soltani a ranar 14 ga Janairu.

A takaice dai, doka ba ta tanadar da hukuncin kisa ga irin wadannan tuhume-tuhumen ba.” Inji ma’aikatar shari’a ta Iran.

Sanarwar ta kara da cewa a halin yanzu Soltani yana tsare a gidan yarin Karaj, wani birni da ke yammacin Tehran.

Bugu da kari, hukumar shari’a ta yi Allah wadai da “kirkirar bayanai marasa tushe” da kafofin watsa labarai na ‘yan adawa masu alaka da kasashen waje suka shirya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted