shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yamen ya fadi cewa kasar Amurka da isra’ila sun aike da wakilansu domin tayar da tarzoma a iran inda suka kona masallatai suka kuma kashe jami’an tsaro , sai dai Alummar iran sun mayar musu da martani ta hanyar shirya gagarumar zanga-zangar ta miliyoyin mutane a fadin kasar.
Sayyid Abdulmalik Badr Din Alhouthi ya yi wadannan bayanan ne a jawabin da yayi a jiya Alhamis a lokacin bukin tunawa da zagayowar shahadar sayyid Hussaini Badr Din wanda ya assasa kungiyar Ansarullah, yace zanga-zangar lumana da aka yi a iran kan matsalar tattalin arziki da ta rikide ta koma tarzoma a makon jiya wanda kalaman da Amurka da isra’ila suka yi ya kara ruruta wutar rikicin.
Mutane dauke da makamai sun lalata dukiyoyin alumma da suka hada da masallatai da sauran kayyakan jama’a, da haka ya haifar da mummunar asararar rayukan fararen hula da jami’an tsaro.
Shugaban kungiyar Ansarullah ya jaddada cewa wadannan makiya sun kai hari kan musulmi ta hanyar kisan gilla da kisan kare dangi da keta mutunci suna neman wulakantasu da kuma bautar da Alumma.