Gwamnatin Tarayya Na Kokari Wajen Gina  Rundunonin Tsaro Masu Karfi Da Inganci

Ministan Tsaron Nigeriya , Janar Christopher Musa mai ritaya, ya jaddada aniyar gwamnatin tarayya na gina ingantattun rundunonin soji, dake cike da Kwararru da kuma

Ministan Tsaron Nigeriya , Janar Christopher Musa mai ritaya, ya jaddada aniyar gwamnatin tarayya na gina ingantattun rundunonin soji, dake cike da Kwararru da kuma juriya, domin kare martabar Nijeriya da kuma tallafa wa wajen ci gaban kasa.

Musa ya bayyana haka ne a wajen bude taron karawa juna sani na kasa, wanda aka shirya; domin tunawa da ranar sojojin kasar na shekarar 2026 a Abuja.

Ya ce, ma’aikatar tsaro a karkashin gwamnatin mai ci, tana ba da fifiko kan jin dadin sojoji da inganta horar da su da koyarwa da kuma fadada samar da tsaro na cikin gida, domin tabbatar da dorewar tsaro na tsawon lokaci.

Haka zalika ya ce, Nijeriya na amfani da wadanda suka samu kwarewa a cikin gida tare kuma da karfafa kirkire-kirkire ta fuskar tsaro da kuma samar da kwarewa.

Game da ayyuka, ministan ya bayyana cewa; ingantacciyar hanyar horar da sojoji ta musamman da kuma karfafa hadin gwiwa tare da abokan huldar yanki da na kasa da kasa, sun inganta musayar bayanan sirri da tasirin aiki, kan barazanar da kasashen duniya ke fuskanta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted