Mededov Na Rasha: Cikin Sauki Kasashen Turai Za Su Mika Wa Amurka Yankin Greenland

Shugaban  Majalisar tsaron kasar Rasha Dmitry Mededov ya ce; Duk da cika bakin da kasashen turai suke yi akan batun Greenland, sai dai abu ne

Shugaban  Majalisar tsaron kasar Rasha Dmitry Mededov ya ce; Duk da cika bakin da kasashen turai suke yi akan batun Greenland, sai dai abu ne mai yiyuwa su mika yankin ga Amurka acikin sauki.

Demitry Mededov wanda yake mayar da martani akan furucin shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron akan cewa idan aka  keta hurumin kasar Denmark, to kuwa za a fuskanci mummunan sakamako.

Mededov ya yi tambaya da harshen turanci yana cewa: “Zakara ya yi cara akan cewa idan aka keta hurumon kasar Denmark, to za a fuskanci mummunan sakamako.”

Zakaran da Mededov yake Magana akansa shi ne alamin kasar faransa.

Shugaban majalisar tsaron kasar ta Rasha ya kara da cewa; Ban san abinda zai faru ba. Shin idan hakan ta faru, za su je su sato shugaban kasar Amurka ne, ko kuwa za su kai harin makamin Nukiliya ne a cikin jam’i?

Mededov ya furta cewa, babu ko daya da zai faru, domin a cikin sauki za su mika yankin na Greenland ga Amurka, da hakan zai shiga cikin tarihin kasashen turai.

Shugaban kasar Amurka ya sha nanata aniyarsa ta shimfida ikon Amurka a cikin yankin Greenland dake a karkashin masarautar Denmark, ta hanyar sulhu ko kuma ta amfani da karfin soja.

Wannan matsalar  ta Amurka ta jefa kasashen turai cikin rudani da kuma rabuwar kawuna akan yadda za su yi da abokiyar kawancensu a karkashin kungiyar Nato.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted