Jami’an ‘yan sandan kasar Habasha sun sanar da kame albarusai 50,000 da su ka ce kasar Eritrea ta aike wa ‘yan tawayen kasar.
A cikin watan Oktoba kasar Habasha ta zargi makwabciyarta Eritrea cewa tana kokarin hargitsa zaman lafiya ta hanyar bai wa masu dauke da makamai kudi,musamman a yankin Amhara.
Sai dai kasar ta Eritrea ta ce, zargin na Habasha babu kamshin gaskiya a cikinsa.
Rundunar ‘yan sandan ta kasar Habasha ta wallafa a shafinta na “facebook” cewa an sami albarusai 56,000 a yankin Amhara aka so ya shiga hannun kungiyar dake dauke da makamai ta “Arm The Fano.” Wannan kungiyar ce dai gwamnatin tarayyar Habashan ta yi yaki da ita a cikin shekarar 2023.
Sanarwar ta ce, an dauko albarusan ne dai a cikin wata babbar mota sun kuma ratso ta yankin Tigray bisa taimakon kungiyar da take dauke da makamai a yankin ta ” Tigray’s People’s Libration Front ( TPLF).
Ita dai wannan kungiyar ta “TPLF” ta shimfida ikonta a yankin na Tigray na lokaci mai tsawo har zuwa 2018, da kuma yakin da ya barke daga 2020 zuwa 2022.
Alaka a tsakanin kasashen Habasha da Eritrea ta yi kamari a bayan nan. Shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki ya ce; jam’iyyar da take Mulki a Habasha ta shelanta yaki akan kasarsa.