Iran Ta Gargadi Trump Kan Kokarin Isra’ila Na Jefa Amurka Cikin Yaki A Madadinta

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi gargadi shugaban Amurka Donald Trump game da kokarin Isra’ila na yin amfani da shi wajen jefa

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi gargadi shugaban Amurka Donald Trump game da kokarin Isra’ila na yin amfani da shi wajen jefa Amurka cikin yakin soji kai tsaye da kasar Iran a madadinta.

Acikin shafinsa na X ministan ya bayyana irin tarihin dabarun halayen gwamnatin sahyuniya na kokarin cimma manufofinta ta hanyar yin amfani da Amurka wajen kare manufofinta a kasashen yankin.

Ministan ya tona asirin gaskiyar inda tarzomar da ta faru a kasar ta samo  asali , yace zanga-zangar baa cikin gida aka kitsa ta ba, an shirya ta ne daga waje yadda za ta yadu a ko ina a cikin kasar. Amma Trump ya san inda ya kamata yaje ya dakatar da kashe –kashe da ake yi.

A yan kwanakin nan Trump ya sha nanata barazanar cewa za su kawo wa iran hari idan ta dauki mataki kan masu tada tarzoma da kashe-kashe da ya kira su da masu zanga-zangar lumana.

Kwamandan dakarun kula da sararin samaniyar na dakarun karun juyin musulunci Brigadier Ganaral Majid Mosavi ya fadi a ranar laraba cewa dakarun su suna cikin kyakkawan shari na tsaro domin dakile duk wani wuce gona da iri kan kasar Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted