Bayan kwashe shekaru 16 ana tattaunawa tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’oi ta Asuu daga karshe dai gwamnati ta amince da karin albashi kashi 40% ga dukkan malaman jami’oi a jamioin gwamnati dake fadin kasar, bayan yarjejeniyar da aka sanyawa hannu tsakanin gwamnti da Asuu.
Ministan ilimi na kasa Dr Tunji alausa shi ne ya bayyana haka a sa’ilin da ake sanya hannun kan yarjejeniyar tsakanin Asuu da gwamnatin Najeriya a birnin trayyar Abuja,
Haka zalika Alausa ya kara da cewa wannan shi ne karon farko acikin tarihin kasar shugaban kasar mai ci ya zama yana da cikakken iko ya fuskanci wannan kalubale da ya dade yana fuskantar fanni ilimi a fadin kasar kuma ya mayar da hankali ga shugabannin wajen kai mu inda muke a yau. Idan ana iya tunawa a shekara ta 2009 gwamnatin nigeriya da kungiyar malaman jami’oi ta Asuu sun rattaba hannu kan yarjeniyar da zimma samar da walwala,kudade, yanci jami’oi, da kuma kaidojin jami’oin gwammatin tarayya, sai dai rashin aiwatar da shirin ya haifar da shiga yajin aiki na tsawon lokaci.