Gwamnatin Sudan ta sanar da yankewar dukkanin hanyoyin samun kudaden shigarta tun bayan fara yakin basasar kasar a watan Afrilun shekara ta 2023 tsakanin dakarun kasar da mayakan RSF wanda yanzu haka ke cika shekaru 3 cif da farawa.
Ministan kula da harkokin kudade na kasar Gibril Ibrahim da yake sanar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na AFP, ya ce, yanzu haka gwamnatin ba ta da hanyoyin samun kudaden tafiyar da harkokin yau da kullum.
Tuni yaki ya yi kaca- kaca da komai a biranen Sudan, bayan da Sojoji suka yi amfani da kudaden da ya ragewa gwamnati wajen tanadin kayan yaki da harkokin sufurinsu don zama cikin shirin ko ta kwana game da hare-haren RSF, yayin da aka rasa hanyoyin tattara kudaden shiga ta bangaren man Fetir da danyen Zinari da kasar ke fitarwa, lamarin da kai tsaye ya jefata a matsanancin halin karyewar tattalin arziƙi.
A wannan makon ma Firaministan Sudan ya bayyana komawar Ofisohin manyan jami’an gwamnatin kasar zuwa Khartoum da Sojin gwamnatin suka sake kwata daga hannun RSF a bara.
Sudan kasa ce mai dimbin arziƙin man fetir da Zinari da fadin kasa mai albarka, amma yanzu kasar na fama da matsaloli da fiye da rabin al’ummarta na dogara ne ga kayan agaji domin rayuwa.