Wata cibiyar bincike mai suna “Frensic Architecture’ ta bada sanarwan cewa, HKI tana fakewa da tsagaita budewa juna wuta a Gaza a matsayin dama ta sake shata kan iyakoki a zirin gaza.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto cibiyar tana cewa a halin yanzu HKI ta maida ‘koren layin da Trump ya shata a shwarar tsagaita wuta da ya gabata na tsaida yaki a Gaza a matsayin sabon taswirar Gaza.
Labarin ya kara da cewa an Trump ya gabatar gabatar da wannan shawarar ce don sake tsuge fadin gaza, wanda kuma a halin yanzi sojojin hki suna hana Falasdinawa a gaza zuwa kusa da layin da suka shata, kuma duk wanda ya matso kusa da shi suka harbeshi.
Labarin ya kara da cewa tun ranar da aka tsagaiya wuta a ranar 10 ga watan Octoban shekara ta 2025 HKI ta mamaye kashe 54% na zirin Gaza inda ta kara rage fadin yankin wanda mutane fiye da miliyon biyu suke rayuwa.