Yawan Falasdinawa Da Suka Yi Shahada Na Karuwa Saboka Keta Yarjeniyar Tsagaita Wuta

Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta bada sanarwan cewa yawan Falasdinawa wadanda sojojin HKI suke kashewa a Gaza yana karuwa duk tare da abinda suka

Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta bada sanarwan cewa yawan Falasdinawa wadanda sojojin HKI suke kashewa a Gaza yana karuwa duk tare da abinda suka kira tsagaiya budewa Juna wuta.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto ma’aikatar na cewa a cikin sa’oii 24 da suka gabata sojojin HKI sun kashe Falasdinawa 2 sannan masu bincike sun gano gawakin mutanen 8 a karkashin burbushin gine-ginen da aka rusa a cikin shekaru 2 da suka gabata.

Labarin ya kara da cewa daga ranar 11 ga watan Octoban shekara ta 2025 ya zuwa yanzu sojojin HKI sun kashe falasdinawa 347 sannan sun raunata wasu 889 wanda ya kara yawan  Falasdinawa da suka yi shahada tun fara yakin tufanul aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 zuwa 69,785 sannan wadanda suka ji rauni kuma zuwa 170,965.

Kungiyoyi masu sa ido na kasa da kasa sun ce ba’a dakatar da kisan kiyashi a gaza ba duk tare da tsagaita wuta. Kuma al-amaran jinkai suna kara tabarbarewa a yankin. Sun kuma bayyana cewa idan wannan halin ya ci gaba mai yuwa yankin ya sake rikicewa.

Wata kungiyar Yahudawa a birnin NewYork ta bayyana cewa yahudawan sahyoniyya sun kashe Falasdinawa 500 a cikin kwanaki 44 da tsagaita wuta a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments