Faransa, Jamus, Italiya, da Burtaniya sun yi tir da “karuwar rikici” a yammacin kogon jodan

Kasashen Faransa, Jamus, Italiya, da Burtaniya sun yi Allah wadai da “karuwar yawan tashin hankalin” da yahudawa ‘yan gudun kama wuri zaman ke yi wa

Kasashen Faransa, Jamus, Italiya, da Burtaniya sun yi Allah wadai da “karuwar yawan tashin hankalin” da yahudawa ‘yan gudun kama wuri zaman ke yi wa fararen hular Falasdinawa, tare da yin kira ga Isra’ila da ta kare al’ummar Yammacin Kogin Jordan.

“Wadannan hare-haren dole ne a daina su.

Suna kawo cikas ga kokarin da ake yi na tabbatar da zaman lafiya da kuma tabbatar da tsaron Isra’ila mai dorewa,” in ji ministocin harkokin waje na kasashen hudu a cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa.

Sun kuma yi maraba da ” bayyanannar adawar” da shugaban Amurka Donald Trump ya nuna kan yunkurin mamaye Yammacin Kogin Jordan kuma sun sake nanata adawarsu “ga duk wani nau’in mamayewa, ko na bangare, ko na gaba daya, ko na zahiri, da kuma ayyukan gina matsugunan da suka saba wa dokokin kasa da kasa.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted