Rahotanni sun nuna cewa hare-haren da Isra’ila ta kai a sansanin yan gudun hijira na Ainul Hilwa dake kusa da Sidon yayi sanadiyar shahadar falasdinawa 22 tare da jikkata wasu da dama, kana sun soki kasar Labanon game da rashin daukar matakin soji da na siyasa akai.
Harin an kai shi ne kan sansanin yan gudun hijira mafi girma dake kasar Labanon yanzu dai dubban gidaje ne suka shiga cikin fargaba saboda da hare haren da isra’ila ke kaiwa ba kakkautawa,
Gwamnatin kasar labanon na fuskantar mummunar suka na rashin daukar matakan da suka dace da haka yasa isra’ila ke yawan kai hare-hare a kudancin kasar, yayain da jami’an gwamnatin ke cewa yanzu haka suna shirin mika wani korafi ga kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya, duk da yake cewa wanda suka aika abaya ma bai yi wani tasiri na a zo a gani ba.
Ministan lafiya na kasar labanon ya tabbatar da cewa harin ya samu yankunan dake kusa da masallacin khalid bin walid da ya kai ga shahadar falasdinawa 22 tare da jikkata wasu da dama, rahotanni su nuna cewa harin da isra’ila ta kai da jirgin sama mara matuki ya sami wata mota da ake zargin wani bangare ne na kisan gilla da take kokarin yi.