Iran Ta yi Gargadi Kan Kada Kudurin Amurka Da MDD Ta Amince Da Shi Ya Tauye Hakkin Falasdinawa  

Rahotanni sun bayyana cewa Iran ta yi suke kudurin Amurka da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya amince da shi na tilasta aikewa da

Rahotanni sun bayyana cewa Iran ta yi suke kudurin Amurka da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya amince da shi na tilasta aikewa da dakarun kasa da kasa zuwa yankin gaza domin tabbatar da zaman lafiya,  ta yi gargadin kada ayi amfani da shi wajen take hakkokin alummar falasdinu na kafa kasarsu mai cin gashin kai

A wani bayani daya fitar tun a ranar talata ma’aikatar harkokin wajen iran ta ce  kudurin da aka amince da shi ya manta da ainihin rawar da majalisar dinkin duniya za ta taka da kuma kudurinta na baya da ya shafi yankin falasdinu.

Kuduri mai lamba 2803 an amince da shi ne a ranar litinin da ta gabata inda ya bukaci kafa dakarun tabbatar da zaman lafiya na kasa da kasa a yankin gaza , karkashin abubuwan 20 da shugaban Amurka Donald trump ya gabatar da yace shirin zai kawo karshen yakin isra’ila da kisan gare dangi da take yi a gaza, da ya fara tun daga watan oktoban shekara ta 2023.

Ma’aikatar ta nuna damuwa matuka game da wannnan kuduri kuma ta jaddada goyon bayanta kan duk wani mataki da zai kawo karshen kisan kare dangin Amurka a yankin Gaza, da isar da kayan agaji da kuma janyewar dukkan sojojin mamaya baki daya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments