Shugabar kasar maziko Claudia shinbaum ta fadi a cewa kasarta ta yi watsi da duk wani kokarin tsoma bakin kasashen wajen da kuma kalaman da shugaban Amurka Donald Trump yayi na kai harin soji kan iyakar kasar.
A farkon makon nan ne trump yace yana so ya umarci sojoji su kaddamar da wani samame a kasar meziko domin yakar masu fataucin miyagun kwayoyi, yace wata dama ce gareshi ya aiwatar da wannan aiki don haka zai yi duk abin da ya dace wajen ganin an kawo karshen masu fataucin miyagun kwayoyi a yankin.
Da aka tambayeshi ko zai nemi izinin kasar Maziko, sai yace ya riga yayi Magana da jami’an gwamnatin meziko sai dai basu gamsu da kokarinsa ba, amma sun san matsayarsa akai,
Shugaban kasar tace a lokuta daban daban shugaban Amurka Trump ya bukaci ya bada taimakon soji a kasar meziko wajen yaki da masu fataucin miyagun kungiyoyi, sai dai ina sake nanatawa cewa ba za mu yi aiki tare ba, na kawo mana wani taimako da ya bukata, zamu ci gaba da kula da iyakokin kasarmu kuma ba zamu taba amincewa da katsalandam din kasashen waje ba.