kungiyar Hadin Guiwa Ta SCO Ta yi Watsi Da Adawar Da Kasashen Turai Ke Nuna wa Kasar Iran

pirme ministocin kungiyar hadin guiwa ta kasashen shangai SCO sun kawo karshen taron kungiyar karo na 24 a birnin mosko inda suka fitar da bayanin

pirme ministocin kungiyar hadin guiwa ta kasashen shangai SCO sun kawo karshen taron kungiyar karo na 24 a birnin mosko inda suka fitar da bayanin hadin guiwa na yi watsi da duk wani mataki na kasashen turai dake nuna adawa da kasar iran, musamman kan abin da ya shafi shirin ta na nukiliya na zaman lafiya.

Bayanin karshe na taron da mamabobin kungiyar suka fitar ya yi tir da adawa da kasashen yamma ke nunawa kasar iran  da ya shafi takunkumin karya tattalin arziki da ya sabama dokokin kasa da kasa , shuwagabannin sun yi gargadin cewa daukar irin wannan matakai zai cutar da majalisar dinkin duniya wajen cimma kudurin ci gaban alumma.

Kasashen Amurka da sauran kawayenta sun maka takunkumai kan kasar iran kan shirinta na naukiliya na zaman lafiya da zargin cewa wai kasar tana neman kera makamin nukiliya, lamarin da iran ta karyata tun tuni.

Iran da Amurka sun gana ba kai tsaye ba har sau 5 a farkon wannan shekara domin sabunta yarjejeniyar da aka cimma a shekara ta 2015 wanda ya hada da kudurin majalisar dinkin duniya dake gab da karewa amma haka ba ta cimma ruwa ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments