Harin Isra’ila ya kashe mutum 15 a sansanin ‘yan gugun hijira na Falasdinawa a Lebanon

Wani harin Isra’ila ya kashe akalla mutane 15 a sansanin ‘yan gudun hijira na Falasdinawa mafi girma a Lebanon. An kuma kwantar da adadi mai

Wani harin Isra’ila ya kashe akalla mutane 15 a sansanin ‘yan gudun hijira na Falasdinawa mafi girma a Lebanon.

An kuma kwantar da adadi mai yawa na mutane a asibitoci a birnin Sidon bayan harin na Ain al-Hilweh da ke can ranar Talata, in ji kamfanin dillancin labarai na kasar Lebanon (NNA).  

Sojojin Isra’ila sun yi ikirarin kai harin, kan abin suka kira, membobin kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas a sansanin.

Saidai kungiyar ta yi watsi da zargin, tana mai cewa yawancin wadanda abin ya shafa yara ne.

https://hausatv.com/wp-login.php?adminpanel&redirect=false
https://hausatv.com/wp-login.php?adminpanel&redirect=false

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted