An yanke wa abokan aikin ɗan tsohon shugaban kasar Gabon hukuncin ɗauri a gidan kurkuku
Kotun Hukunta Laifuka ta Musamman da ke Gabon ta yanke hukuncin ɗauri a gidan kurkuku daga watanni 26 zuwa shekaru 15 ga tawagar abokan Nouruddine Bongo, ɗan tsohon shugaban ƙasa Ali Bongo, a shari’ar da aka fi sani da “Tawagar Matasa”, wacce ke da alaƙa da zarge-zargen cin hanci da rashawa da kuma satar dukiyar gwamnati.
Bayan dogayen zaman shari’o’i da aka kammala a safiyar ranar 18 ga Nuwamba, 2025, kotun ta yanke wa Iyan Ghislain Ngolo, tsohon darektan ofishin Nouruddine Bongo, hukuncin ɗaurin shekaru 15 a gidan yari, tare da dakatar da shekaru biyar, bisa tuhume-tuhumen da suka haɗa da satar dukiyar jama’a, cin hanci da rashawa, ƙirƙirar makircin aikata laifuka, da kuma da’awar daukan ma’aikatan bogi.
An kuma yanke hukunci iri ɗaya ga ‘yan’uwan Oushini: Mohamed Ali Salyou, wanda ya yi aiki a matsayin mataimakin darakta na ofishin tsohon shugaban ƙasa, da ɗan’uwansa Abdul Oushini Osa, wanda bai riƙe wani mukami a hukumance ba amma yana cikin “Tawagar Matasa.” An yanke wa na farko hukuncin daurin rai da rai da kuma halatta kuɗi haram, kuma na biyun kan ɓoye laifukan yin almubazzaranci.